Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan haraji da wasu kudade da ake biya ya ragu da Yuan triliyan 1.5 a farkon rabin shekarar bana a kasar Sin
2020-08-07 13:32:07        cri

Jiya Alhamis, rukunin nazari na ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta ba da rahoto kan yadda aka gudanar da manufofin kudi a farkon rabin shekarar bana, karon farko dama'aikatar ta gabatar da irin wannan rahoto.

Rahoton ya nuna cewa, a farkon rabin shekarar bana, tattalin arzikin kasar Sin ya dan samu koma baya, daga baya kuma ya farfado. Daga watan Afrilu zuwa watan Yuni, an rika samun kyautatuwa a fannin tattalin arziki a mataki-mataki, inda wasu manyan mizanai suka yi ta karuwa.

Alal misali, yawan haraji ko kudin da aka biya ya ragu fiye da kudin Sin RMB Yuan triliyan 1.5, kuma an ci gaba da rage haraji da kudi da da ake biya a bana. Matakan da ake dauka sun hada da mayar da haraji ko kudin da kamfanoni masu samar da kayayyakin kandagarki suka biya, da kuma tallafawa kananan kamfanoni ko 'yan kasuwa masu zaman kansu don su tinkari mawuyancin hali. Tun daga lokacin da aka aiwatar da manufar rage buga haraji, kamfanoni da kuma daidaikun mutane miliyan 1.91 sun ci gajiya. Matakan rage kudin inshorar al'umma da kamfanoni za su biya, zai kawar da matsin lambar da suke fuskanta a fannin kudade. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China