Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin zata inganta manufar rage harajin da ake biya a shekarar 2020
2020-01-07 10:19:59        cri
Kasar Sin zata dauki karin matakai a shekarar 2020 domin fadada nasarorin da ta cimma a fannin rage kudaden haraji da ma sauran kudaden da ake biya, hukumar gudanar da al'amurran harajin kasar ce ta bayyana hakan.

Cikin bayanin da ta wallafa a shafinta na intanet bayan gudanar da taro na kasa kan batun harajin a ranar Litinin, hukumar ta ce, za'a kara kaimi wajen inganta yanayin biyan kudaden haraji, da kara ingancin aikin hukumar karbar harjin, da kara zurfafa yin hadin gwiwa da kasa da kasa kan batun na biyan haraji.

A shekarar 2019, kasar Sin ta bullo da manufar rage haraji da ma sauran kudaden da ake biya. Sabuwar manufar da aka bullo da ita ta rage kudaden harajin da aka biya da sama da yuan triliyan 2(kwatankwacin dalar Amurka biliyan 287), wanda ya zarta kashi biyu bisa 100 na GDP din kasar, kana ya samar da gudunmowar kashi 0.8 bisa 100 na bunkasuwar GDP.

Wang Jun, shugaban hukumar gudanar da al'amurran harajin kasar, yace manufar ya haifar da ingantuwar al'amurran kasuwanci kana ya kara samar da kwarin gwiwar samun cigaban tattalin arziki.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China