2019-08-23 20:51:30 cri |
A sabili da haka, kasar Sin ta mayar da martani, inda bisa ga amincewar majalisar gudanarwar kasar, kwamitin tsara dokokin haraji karkashin majalisar ya tsai da kudurin kara sanya harajin da ya kai kaso 10% da kaso 5% a kan wasu kayayyakin Amurkar da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 75 da take shigowa daga kasar ta Amurka, kuma matakin zai fara aiki ne kan rukuni na farko na kayayyakin daga ranar 1 ga watan Satumba mai zuwa, kana daga ranar 15 ga watan Disamba matakin zai fara aiki kan rukuni na biyu na kayayyakin.
Har wa yau, tun daga ranar 15 ga watan Disamban bana, da misalin karfe 12, za ta maido da harajin da ya kai kaso 25% da kaso 5% a kan motoci da kayan gyaran motoci da take shigowa daga kasar.
Kasar Sin ta dauki wannan mataki ne domin mayar da martani kan matakan kariyar ciniki da Amurka ke dauka, kuma kasar Sin ta sake jaddada cewa, hadin gwiwa shi ne hanya daya kacal da kasashen biyu za su iya bi, domin tabbatar da kyakkyawar makomar juna.(Lubabatu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China