Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zargin kasar Sin kan asalin COVID-19 ba zai magance matsalolin Amurka ba
2020-07-20 20:46:19        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya ce, yadda sakataren harkokin wajen Amurke Mike Pompoe ke dorawa kasar Sin laifin asalin kwayar cutar COVID-19 da siyasantar da batun annobar, ba shi zai magance matsalolin da Amurka ke fama da su ba,

Wang na wannan kalamin ne, yayin da yake mayar da martani kan kalaman baya-bayan da Mike Pompeo ya yi game da kasar Sin. Kasar Sin na fatan bangaren Amurka zai nuna halin ya kamata kan rayuka da lafiyar al'ummominta, ta kuma mayar da hankali da ma karfinta wajen yaki da annobar a cikin kasarta, kana ta karfafa alakar kasa da kasa. A don haka, ba daidai ba ne ta rika sukar WHO ko kasar Sin da tunanin da ba shi da tushe. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China