![]() |
|
2020-07-21 21:16:28 cri |
Hukumar kula da harkokin ciniki da bunkasuwa ta MDD wato UNCTAD ta yi hasashen cewa, yawan jarin da 'yan kasuwan waje za su zuba kai tsaye a duniya daga shekarar 2020 zuwa 2021 zai ragu da 30% zuwa 40%, sakamakon barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19. Amma yawan jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da shi a zahiri daga watan Afrilu zuwa watan Yuni a bana ya karu da 8.4% bisa makamancin lokaci na shekarar bara, lamarin da ya nuna cewa, ya zuwa yanzu kamfanoni na alla-alla wajen zuba jari a kasar Sin. Dalilan da suka sa haka su ne domin kasar Sin ta raya tattalin arzikinta yadda ya kamata, tana kuma kyautata yanayin kasuwanci, sa'an nan tana ci gaba da kokarin kara bude kofarta ga kasashen ketare.
Yanzu haka annobar tana yaduwa a duniya. Duk da kalubale da matsin lamba gami da rashin tabbas da kasar Sin take fuskanta wajen tabbatar da ci gaban cinikin waje. A shirye take wajen tunkarar duk wata barazana daga waje cikin dogon lokaci. Kana tana da aniya da kwarewa wajen ci gaba da jawo jarin waje, tare da samar wa duniya damar ci gaba. (Tasallah Yuan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China