Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi:Masu jarin waje suna sha'awar kasuwar kasar Sin
2019-11-27 20:59:21        cri

Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya rubuta wani sharhi yau cewa, hukuma mafi girma a duniya dake bayani kan alkaluman hannayen jari na kasa da kasa na MSCI, ya kara kason kasuwar manyan hannayen jarin kasar Sin a hukumance. A baya kamfanin S&P Dow Jones Indices da na FTSE Russell su ma sun kara mai da hankali kan kasuwar manyan hannayen jarin kasar Sin. Hakan ya nuna cewa, masu jarin waje suna sha'awar kasuwannin hannayen jarin kasar Sin. Masu zuba jari na kasa da kasa kuma suna kara karfin imaninsu kan kasuwannin hannayen jarin kasar Sin.

Yadda jarin waje suke kwarara zuwa kasuwannin hannayen jarin kasar Sin ya nuna cewa, masu zuba jari na kasa da kasa sun nuna imani kan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, haka kuma, hakan zai taimaka wajen kyautata tsarin masu zuba jari a kasuwannin kasar Sin, ta yadda za a ba da jagora kan samar da tunanin zuba jari cikin dogon lokaci a kasuwa.

Sharhin ya yi nuni da cewa, kasuwannin jarin kasar Sin zai samar wa masu zuba jari na duniya karin damammaki, za su kuma ci gaba da kara kokari kan ci gaban tattalin arzikin duniya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China