![]() |
|
2020-05-06 16:44:54 cri |
A sa'i daya kuma, an samu karin mutanen da suka yi sayayya a shaguna, bisa wasu matakan da aka dauka domin habaka bukatun al'umma.
Haka kuma, mun ga nasarorin da aka samu wajen kare lardin Hubei gami da birnin Wuhan, kasar Sin ta cimma sakamako mai kyau wajen dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, ta yadda al'ummomin kasar za su iya tafiya yawon shakatawa a wuraren kasar cikin kwanciyar hankali a yayin hutun Ranar Ma'aikata Ta Duniya. Cikin watanni uku da suka gabata, jam'iyyar kwaminis mai mulki da gwamnatin kasar Sin sun dauki matakai yadda ya kamata, dubban ma'aikatan lafiya sun dukufa wajen samar da jinya, Sinawa sama da biliyan 1.4 sun martaba dokar zama a gida yadda ya kamata, lamarin da ya sa kasar Sin ta zama kasa ta farko da ta yi nasarar dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a cikinta. Al'ummar Sinawa sun ji dadin wannan hutun na watan Mayu bisa kokarin da suka yi.
A matsayinta na kasar da ta ba da gudummawar kaso 30 cikin 100 na karuwar tattalin arziki na duniya, kasar Sin ta dakile yaduwar cutar yadda ya kamata, ta kuma gaggata dawowa bakin aiki, lamarin da ya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Kwanan baya, jaridar Financial Times ta kasar Burtaniya ta wallafa wani sharhi dake cewa, daya daga cikin dalilan da ya sa babbar karuwar kasuwar hannayen jari ta kasar Amurka a watan Afrilu shi ne, masu hannayen jari suna da imani kan karfin kasar Sin na jagorantar farfadowar tattalin arzikin duniya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China