Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabon jigon ci gaban kasar Sin zai kara azama kan hadewar duniya da cudanyar juna
2019-09-25 20:30:48        cri

Yau Laraba ne shugaba Xi Jinping ya sanar da fara aiki da filin jiragen sama na kasa da kasa na Daxing na Beijing a hukumance, wanda ke matsayin sabuwar alamar Beijing, da ta kasar Sin, kuma muhimmiyar tasha ta hada hanyoyin sassan duniya a nan gaba.

Filin jiragen saman na kasa da kasa na Daxing, zai kasance sabon jigo a fannonin bunkasa kasar Sin, da kara azama wajen hade kasashe da yankunan da suka aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", da cudanyar juna a tsakaninsu.

Filin jiragen saman na kasa da kasa na Daxing, ya nuna yadda kasar Sin take raya kasa bisa tunanin yin kirkire-kirkire, da mayar da mutane a gaba da komai, da bude kofa ga kowa ba tare da gurbata muhalli ba, matakin da ya samu amincewa sosai a gida da wajen kasar Sin.

Sufuri, muhimmin jigo ne na bunkasa birane. Filin jiragen saman na kasa da kasa na Daxing, wanda ya fara karbar fasinjoji a yau, zai zama sabon jigon ci gaban kasar Sin, kuma tabbas zai kara babban kuzari ga hadewar duniya da cudanyar juna. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China