Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jam'iyyar kwaminis ta kasar Afrika ta kudu ta amince da matsayin da Sin ta dauka kan yankin Hongkong
2020-06-29 19:59:12        cri

Mataimakin sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Afrika ta kudu na biyu Solly Mapaila ya shedawa manema labarai a kwanan baya cewa, jam'iyyarsa na goyon bayan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kuma ta amince da matsayin da Sin ta dauka kan yankin Hongkong da nuna adawa da duk wani yunkurin kawo baraka a kasar Sin. Jam'iyyar ta kuma yi Allah wadai da ayyukan kawo baraka a Hongkong da aka aiwatar a yankin karkashin goyon bayan wasu kasashen yamma da hukumomi, a ganinsa, duk wani mataki na shisshigi a harkokin cikin gidan kasar Sin ba zai samu nasara ba ko kadan. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China