Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dokar Tsaron HK Za Ta Farfado Da Yankin
2020-05-27 15:22:40        cri
A yayin taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin dake gudana a halin yanzu, ana dudduba daftarin tsarawa da inganta dokar kiyaye tsaron kasa ta yankin musamman na Hong Kong gami da tsarin aiwatar da ita, daftarin da ya samu goyon bayan al'ummomin yankin na Hong Kong.

Sassa daban daban sun sa hannu kan Internet da kuma a zahiri domin mara baya ga daftarin dokar. Ya zuwa ranar 26 ga wata, wato kwanaki uku kawai mutane fiye da miliyan 1 da dubu 100 sun sa hannu, lamarin da ya nuna cewa, daftarin dokar ya haskaka makomar yankin musamman na Hong Kong.

Hakika dai, samun jituwa da kwanciyar hankali, babban buri ne na al'ummar Hong Kong. Al'ummomin yankin suna matukar bukatar a kwantar da kura da kawo karshen tashin hankali. Tsarawa da kyautata dokar kiyaye tsaron kasa ta Hong Kong da tsarin aiwatar da ita ya dace da muradun yankin musamman na Hong Kong da ma kasar Sin, kana kuma zai amfana wajen kiyaye halaltattun hakkokin jama'ar yankin da kuma 'yancinsu, lamarin da ya sa ya samu amincewa daga al'ummar yankin. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China