2020-06-05 10:48:32 cri |
Allegra Baiocchi, shugabar kula da shirin bada agaji ta MDD a Kamaru ta ce, watanni biyun da suka gabata an samu karuwar hare haren inda aka bada rahoton hukumomin agaji shida anyi garkuwa da jami'ansu, ko kuma an tsaresu tare da yiwa rayuwarsu barazana.
Baiocchi ta fada cikin wata sanarwa da aka fitar a birnin Yaounde na kasar cewa, lamarin ya kai wani mataki inda masu aikin bada agajin sun shiga wani yanayi na rashin tabbas game da makomar rayuwarsu.
A cewar sanarwar, galibin garkuwar da mutane da ake samu, mayakan 'yan aware ne suke aikatawa, sannan dakarunn gwamnati suna fuskantar jinkiri wajen shigar da kayan agajin zuwa yankunan.
Jami'ar tayi gargadin cewa, hare haren da ake kaddamarwa kan ma'aikatan bada agajin ba za'a aminta ba tilas ne a kawo karshensa. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China