Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamaru ta bullo da shirin sake gyaran yankunan magana da Turanci dake fama da rikici
2020-04-16 15:12:44        cri

Firaministan jamhuriyar Kamaru Joseph Dion Ngute, ya sanar cewa, gwamnatin kasar ta bullo da shirin sake gyaran yankunan kasar biyu masu magana da yaren Turanci bayan mummunar barnar da yankunan suke fuskanta na rikicin mayakan 'yan aware a tsawon shekaru uku.

Ngute ya ce, ayyukan gyarawa sun hada da gyaran makarantu kimanin 350, da asibitoci 115, da gadoji 40, da tashoshin samar da ruwan sha 400, da hanyoyin mota a yankunan karkara masu nisan kilomita 600, da kasuwanni 45, da gonakin noma masu fadin murabbi'in mita 25,000, da kafa gonakin kiwon dabbobi.

Ngute ya yi tsokacin ne a babban birnin kasar, Yaounde, a lokacin bikin nada mambobin hukumar da za ta jagoranci aiwatar da shirin.

Ya ce, za'a fara gudanar da aikin ba tare da bata lokaci ba a yankunan da ake da zaman lafiya da kwanciyar hankali.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China