Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mayakan BH sun kashe fararen hula biyu a yankin arewa mai nisa na Kamaru
2020-04-22 09:56:01        cri
An kashe akalla fararen hula 2, yayin wani hari da kungiyar BH ta kai yankin arewa mai nisa na Kamaru a ranar Litinin da daddare.

Majiyoyi daga yankin sun ce mayakan sun farwa kauyen Talla na yankin Mora, inda suka cinnawa gidaje wuta tare da kashe wasu maza 2 da suka yi yunkurin gudu.

Dairou Mohammed, wani dan jarida dake yankin, ya shaidawa Xinhua cewa, mayakan sun kuma sace kayayyakin mazauna kauyen, kana sun yi barazanar komawa su kashe su baki daya, idan suka sanar da lamarin ga jami'an tsaro.

A baya-bayan nan, kungiyar BH ta addabi yankin arewa mai nisa na Kamaru, wanda ke iyaka da Nijeriya da Chadi, inda take kai hari kan fararen hula.

Tun bayan da BH ta kaddamar da kai hari yankin a shekarar 2014, ayyukanta sun yi sanadin mutuwar mutane sama 2,000. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China