2020-05-04 10:49:28 cri |
Kingsley Ashu, shugaban 'yan arewa shi ne ya sanar da mutuwar Alhaji a shafinsa na Facebook.
Hukumomin yankin sun ce an kashe kwamandan ne bayan hare haren da sojojin kasar suka shafe mako guda suna kaddamarwa a yankin, lamarin da ya yi sanadiyyar kwace makaman yaki da tarwatsa sansanoni masu yawa na mayakan 'yan awaren.
Alhaji yana jagorantar daya daga cikin manyan rundunonin mayakan 'yan awaren wacce aka fi sani da "Seven Katta Bafut Defence forces" dake yankin, kamar yadda jami'an tsaron kasar suka bayyana.
An ayyana shi a matsayin madugun 'yan ta'adda a shekarar 2018 bayan da ya jagoranci yin garkuwa da dalibai 'yan makaranta su 80 tare da malamansu da direban motar makarantar sakandaren dake Bamenda, birni mafi girma a yankin masu magana da yaren Turanci, majiyar jami'an tsaron ta kara da cewa, kawar da kwamandan daga doron kasa zai iya zama babban koma baya ga mayakan 'yan awaren a yankin.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China