Dakarun gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDD sun kwace filin jiragen saman kasa da kasa na Tripoli
Mai magana da yawun dakarun gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDD Mohamed Gonono, ya bayyana cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai cewa, sun yi nasarar kwace filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa, dake kudancin birnin Tripolin kasar Libya, daga hannun sojojin dake gabashin kasar, a daidai gabar da sassan biyu ke ci gaba gwabzawa.
Gonono ya ce, dakarunsu sun 'yantar da filin jiragen saman, sun kuma tusa keyar dakarun Haftar, kwamandan sojojin dake gabashin kasar, zuwa bin Ghashir dake gabashin filin jiragen saman.(Ibrahim)