2020-05-06 11:52:56 cri |
Yao Shaojun, mai rikon mukamin mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya ce kamata yayi dukkan bangarorin dake yaki da juna a Libya su sanya bukatar kasa sama da komai kuma su baiwa rayuwar mutane muhimmanci fiye da komai kana su yi kokarin tabbatar da tsakaita bude wuta mai dorewa ba tare da bata lokaci ba. Bisa la'akari da halin da ake ciki a yanzu, mutanen kasar Libya sun cancanci samun yanayin zaman lafiya a kasar don tabbatar da yaki da annobar COVID-19 da ake fama da ita a duk duniya.
Yao, ya ce kasar Sin tana taimakawa kasar Libya kuma tana goyon bayan amfani da matakan siyasa don warware rikicin kasar, kuma tana karfafawa MDD gwiwa da kungiyoyin shiyya kamar kungiyar tarayyar Afrika da gamayyar kungiyar kasashen larabawa da su cigaba da aikin shiga tsakani domin samar da fahimtar juna.
Ya ce a ko da yaushe kasar Sin ta yi amanna cewa tilas ne a warware batun takaddamar kasar Libya ta hanyar matakan siaysa. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China