Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
GNA a Libya ta zargi sojoji masu sansani a gabashin kasar da hallaka fararen hula a Tripoli
2020-03-09 10:23:54        cri
Gwamnatin hadin kan kasar Libya (GNA) mai samun goyon bayan MDD ta sanar a ranar Lahadi cewa sojojin kasar masu adawa da gwamnatin dake da sansaninsu a gabashin kasar sun kaddamar da hare hare a wata unguwar da ke birnin Tripoli, inda suka kashe tare da jikkata fararen hula masu yawa.

Sanarwar da gwamnatin GNA ta fitar ta bayyana cewa an kashe wani mutum guda da wata mata kana an raunata wasu mutanen 4 a sakamakon farko na yawan mutanen da aka kashe a harin makami mai linzami wanda mayakan dake biyayya ga babban kwamandan sojojin dake da sansani a gabashin kasar (Khalifa) Haftar suka kaddamar a yankin Suk al-Juma.

Kawo yanzu dai sojojin dake gabashin kasar ba su ce uffan ba game da hare haren.

Kakakin sojojin gwamnatin GNA, Mohamed Gonono, yace dakarun sojojin gwamnati sun kaddamar da hare hare a sassan sojoji masu sansani a gabashi da ke a shiyyar kudancin birnin Tripoli, inda suka tarwatsa rumbun ajiyar albarusai.

Sojojin dake da sansani a gabashin kasar sun sha kaddamar da hare haren soji tun a watan Afrilun shekarar 2019 a yankunan birnin Tripoli da kewaye, da nufin kifar da gwamnatin GNA dake samun goyon bayan MDD wanda firaminsita Fayez al-Sarraj ke jagoranta.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China