Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar dokokin gabashin Libya ta yi tir da mummunan harin da aka kai lardin Sinai na Masar
2020-05-02 15:55:53        cri
Majalisar dokokin Libya mai mazauni a gabashin kasar, ya yi tir da mummunan harin da aka kai yankin Sinai na Masar, da ya yi sanadin mutuwar sojoji 9.

Sanarwar da majalisar ta fitar, ta ruwaito kwamitin kula da harkokin wajen majalisar, na yin tir da kakkausar kalamai, kan harin da aka kai wa sojojin Masar a birnin Bir al-Abd na arewacin Sinai.

Sanarwar ta ce kwamitin na amfani da wannan dama, wajen bayyana goyon bayan majalisar ga majalisar dokoki da gwamnati da al'ummar kasar Masar, kuma a shirye take ta hada hannu da ita wajen yaki da matsalolin dake barazana ga kwanciyar hankali da ci gaba tsakanin al'ummomi.

A ranar Alhamis ne wani bam ya tashi a arewa maso gabashin lardin arewacin Sinai na kasar Masar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji 9. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China