Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkaluman kirkire-kirkiren Sin sun kai matsayi na 14 a duniya
2020-05-20 11:25:15        cri
Yawan kudin da aka kashe wajen yin nazari da bunkasuwa a fannin zamantakewar al'ummar kasar Sin a shekarar 2019 ya kai Yuan triliyan 2.17, wanda ya kai kashi 2.19 cikin dari na adadin GDP na kasar. Ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Wang Zhigang, shi ne ya bayyana haka a gun taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar a jiya.

Wang Zhigang ya bayyana cewa, binciken da hukumar 'yancin mallakar fasaha ta duniya wato WIPO ta gudanar, ya nuna cewa, yawan kirkire-kirkiren da Sin ta yi ya kai matsayi na 14 a duniya, an kuma inganta karfin yin kirkire-kirkire na kasar Sin, kana an samu babban ci gaba kan gina kasar mai kokarin yin kirkire-kirkire.

A halin yanzu, kasar Sin tana fuskantar matsalolin rashin daidaito kan samun bunkasuwa. Muddin ana bukatar samun bunkasuwa mai inganci, akwai bukatar a inganta kimiyya da fasaha, don ta yadda za su samar da gudummawa ga bunkasa kasar a dukkan fannoni, da kyautata zaman rayuwar jama'a, da kuma tabbatar da tsaron kasar baki daya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China