2020-03-24 13:50:37 cri |
Yau Talata ne, da misalin karfe 11:43 na safe, agogon birnin Beijing na kasar Sin, kasar ta Sin ta yi nasarar harba sabbin taurarin dan-Adam da ake iya sarrafawa zuwa sararin samaniya daga cibiyar harba taurarin dan-Adam ta Xichang dake lardin Sichuan a yankin kudu maso yammacin kasar Sin.
An yi amfani da rokar Long March-2C wajen harba wadannan taurarin dan-Adam, kuma suna daga rukunin Yaogan-30. Sun kuma shiga falaki kamar yadda aka tsara.
Wadannan taurarin dan-Adam za su yi aiki da maganadisu wajen gano yanayin muhalli da gwaje-gwajen da suka shafi fasahohin kere-kere.
Wannan shi ne na karo na 329 da aka yi amfani da rokar Long March wajen harba taurarin dan-Adam zuwa sararin samaniya. (Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China