Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a kammala gina tashar sararin samaniyar Sin zuwa shekarar 2022
2020-05-06 11:55:23        cri
Jiya Talata, an cimma nasarar aikin zirga-zirga na rokar Changzheng samfurin CZ-5B, wadda aka kera domin shirin gina wata tashar sararin samaniya mai dauke da mutane. Wannan shi ne aikin zirga-zirga a sararin samaniya na farko a lokacin da ake gina tashar sararin samaniya a kan hanyar kewaye.

Mataimakin shugaban sashen kumbon dake dauke da mutane Ji Qiming ya bayyana cewa, bisa shirin da aka tsara, za a kammala aikin gina tashar sararin samaniya zuwa shekarar 2022, kuma za a gudanar da ayyukan zirga-zirga guda 12.

Ya ce, bayan aikin da aka kammala a jiya, za a ci gaba da harba cibiyar sashen kumbo ta Tianhe, da sashen kumbo na gwaje-gwaje na Wentian da sashen kumbo na gwaje-gwaje na Mengtian, da kuma gina manyan wuraren tashar sararin samaniya a kan hanyar kewaye. A sa'i daya kuma, za a harba kumbuna masu dauke da mutane na Shenzhou guda hudu da kuma kumbuna masu dauke da kayayyaki na Tianzhou guda hudu, domin sauyin 'yan sama jannati da kuma samar musu kayayyakin da suke bukata.

Bugu da kari, Ji Qiming ya ce, an riga an zabi 'yan sama jannatin ko-ta-kwana wadanda za su gudanar da ayyukan zirga-zirga a sararin samaniya sau hudu, a lokacin da ake gina tashar sararin samaniya. Kuma yanzu, ana ba su horo. Ban da haka kuma, ya zuwa tsakiyar bana, za a gama aikin zaben 'yan sama jannati rukuni na 3. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China