2020-05-20 11:07:35 cri |
Ma'aikatar kula da ayyuakn kimiyya da fasaha ta kasar Sin, ta ce kasar na daukar batun raya fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI da muhimmanci, inda ta zuba makudan kudade wajen samar da sabbin fasahohin na AI.
Darakta janar na sashen kula sabbin fasahohin zamani na ma'aikatar, Qin Yong, ya ce kasar Sin ta kaddamar da wasu muhimman ayyuka 2 kan sabbin fasahohin AI, inda jarin da za ta zuba ya kai yuan biliyan 1, kwatankwacin dala miliyan 140.7.
A cewar Qin Yong, muhimman ayyukan za su mayar da hankali ne kan fasahohin AI, wadanda su ne bangaren fasaha ta zamani a duniya, da kuma suka dace da muhimman bukatun kasar.
Baya ga zuba jari a muhimman ayyukan 2, ma'aikatar ta kaddamar da jerin matakan bunkasa ci gaban fasahar AI.
Ya ce a mataki na gaba, ma'aikatar za ta karfafa tallafawa raya fasahohin AI ta hanyar inganta bincike da muhimman fasahohi, da kuma karfafa dabarun aiki domin samar da ci gaba mai aminci. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China