Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Motar binciken duniyar wata ta kasar Sin ta yi tafiya fiye da tsawon mita 357 a duniyar wata mai nisa
2020-01-03 14:02:42        cri

 

Motar binciken duniyar wata ta kasar Sin, mai suna "Yu Tu 2", ta yi tafiya a doron duniyar wata mai nisa, wadda tsawonta ya kai mita 357.695, domin gudanar da wasu ayyuka na bincike.

Cibiyar gudanar da shirin nazarin sararin samaniya da duniyar wata, ta hukumar binciken sararin samaniya ta kasar Sin ta nuna cewa, na'urorin na tafiya yadda ya kamata, bayan sun isa duniyar wata, inda motar binciken ta yi nazari kan wasu wurare, tare da daukar hotuna kan wani dutse dake fuskar duniyar wata, gami da yin bincike kan wannan dutse ta hanyar amfani da wani nau'in haske.

An ba da labarin cewa, a ran 8 ga watan Disamba na shekarar 2018, Sin ta harba na'urar bincike ta Chang E 4, wadda ta isa kwarin Von Karman dake duniyar wata mai nisa, a ranar 3 ga watan Janairu na shekarar 2019. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China