2020-05-11 13:07:30 cri |
A ranar 7 ga wata, jaridar The Standard ta kasar Kenya, ta wallafa sharhin babban jami'in sakatariyar majalisar raya wuraren yankin iyaka na kasar Mohamed Guleid, inda ya bayyana cewa, zargin da kasar Amurka ta yi wa kasar Sin kan asalin cutar COVID-19, ya nuna cewa, kasar Amurka tana son tada yaki tsakaninta da kasar Sin. Ya kara da cewa, ainihin sabanin dake tsakanin Sin da Amurka ba cutar COVID-19 ba ce, batu ne na bunkasuwar kasar Sin cikin sauri.
Har wa yau, manyan kafofin yada labarai na kasashen Afirka da suka hada da kamfanin dillancin labaran kasar Habasha, jaridar Punch ta Najeriya, da gidan talabijin na kasar Afirka ta Kudu da sauransu, sun mai da hankali kan jayayyar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, kan batun asalin cutar numfashi ta COVID-19, inda suka kuma jaddada cewa, gwamnatin kasar Amurka ta yiwa kasar Sin wannan zargi a daidai lokacin da ake zarginta kan gaza yin aikin dalike yaduwar cutar yadda ya kamata, shi ya sa, 'yan adawar gwamnatin kasar Amurka sun nuna cewa, Donald Trump yana zargin kasar Sin ne kawai, domin dauke hankalin jama'ar kasarsa.
Haka kuma, jaridar Leadership ta Najeriya, da jaridar The Reporter ta kasar Habasha, da kamfanin dillacin labaran kasar Habasha, da jaridar The Star ta kasar Afirka ta Kudu, da wasu manyan kafofin watsa labaran kasashen Afirka, sun yi kira da a karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka wajen yaki da cutar. (Maryam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China