Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cibiyar nazarin kasar Sin dake Najeriya ta jaddada muhimmancin yaukaka zumunta tsakanin kasashen biyu
2020-04-29 11:01:17        cri
Jaridar Daily Trust ta Najeriya, ta wallafa wani rahoto dangane da taron karawa juna sani da cibiyar nazarin kasar Sin dake Najeriyar ta shirya kwanan nan, mai taken "hadin-gwiwar Najeriya da Sin: raya al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya", taron da ya jaddada muhimmancin hadin-gwiwar dake kasancewa tsakanin kasashen biyu, da yin kira ga al'ummar Najeriya, su kare zumunci tsakanin kasashen biyu.

Rahoton ya ruwaito maganar shugaban cibiyar, Mista Charles Onunaiju na cewa, akwai kamanceceniya da dama tsakanin Najeriya da Sin, kuma dangantakarsu na cikin wani yanayi mai kyau. Ya ce an cimma dimbin nasarori wajen gudanar da hadin-gwiwa tsakanin kasashen biyu, al'amarin da ya taimaka sosai ga habakar huldodinsu yadda ya kamata.

Mista Onunaiju ya bayyana cewa, alakar kasashen biyu na da muhimmancin gaske, kana, bai kamata rikicin da ya kunno kai sakamakon matakan wucin gadin da aka dauka na dakile cutar COVID-19 ya kawo illa ga dangantakarsu ba, kuma bai kamata a lalata hadin-gwiwar Najeriya da Sin ba. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China