Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Nijeriya: dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka ba za ta lalace ba saboda wata matsala da suka gamu da ita a wani lokaci
2020-04-30 11:54:45        cri

A ranar 28 ga wata, Jaridar The Nation ta kasar Nijeriya ta wallafa sharhin da masanin cibiyar nazarin harkokin zaman lafiya da warware sabani ta kasar Nijeriya Olalekan A. Babatunde ya rubuta mai taken "Batun Guangzhou ba zai bata dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ba". A cikin sharhin ya bayyana cewa, tarihin Sin da Afirka mai kama da juna da kokarin da suka yi cikin hadin gwiwa domin neman ci gaba suka sa Sin da Afirka sun kulla zumunci mai zurfi. A halin yanzu, hadin gwiwar da Sin da Afirka suka yi kan harkokin tsara shawarar "ziri daya da hanya daya" da aiwatar da sakamakon taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka na Beijing yana ci gaba da inganta hadin gwiwa da dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. Shi ya sa, ya jaddada cewa, zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka yana da dogon tarihi, ba zai lalace ba saboda wata matsalar da suka gamu da ita a wani lokaci. Kuma tabbas ne, za su yi hadin gwiwa wajen warware dukkanin kalubalolin da suka fuskanta yadda ya kamata.

Haka kuma, ya ce, aikin yin kandagarki da hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 da aka yi a birnin Guangzhou, wadda ta shafi al'ummomin kasashen Afirka dake kasar Sin, ta zama wani karamin kalubale cikin hadin gwiwar Sin da Afirka, ya kamata Sin da Afirka su hada kansu wajen warware wannan kalubale, ta yadda za a ci gaba da inganta hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China