Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan kasa da kasa sun musunta labarin dake cewa wai cutar COVID-19 ta fito daga dakin gwaji na Wuhan
2020-05-04 15:21:25        cri

Bayan da cutar COVID-19 ta barke a duniya, wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya da 'yan siyasarsu sun yi hadin gwiwa da raina ilmin likitanci don watsa labarun wai cutar tana da nasaba da cibiyar nazarin kwayoyin cututtuka ta birnin Wuhan na kasar Sin.

Amma masanan kimiyya da kuma masu ruwa da tsaki na kasa da kasa sun yi amfani da ilminsu tare da yin watsi da ra'ayin 'yan siyasar, da rashin gaskiyar ra'ayin da kuskurensu, kana sun kara yin bincike da jaddada cewa, cutar COVID-19 ta fito ne daga halittu.

Kakakin hukumar kiwon lafiya ta duniya ta bayyana a kwanakin baya cewa, a halin yanzu, ana samun wasu ra'ayoyi da ba su da tushe game da asalin cutar COVID-19 a kafofin watsa labaru ko shafukan internet, amma bisa shaidun da aka samu a yanzu, an ce cutar ta fito daga dabba, mafi yiwuwa ne ta zo daga Chiroptera, ba dakin gwaji dan Adam ya kirkiro ba.

A ranar 26 ga watan Maris a bana, shugaban kwalejin nazarin kiwon lafiya na kasar Amurka Francis Collins ya taba gabatar da bayani, inda ya nuna goyon baya ga ra'ayin rukunin nazarin kasa da kasa bayan da aka tantance kididdigar wasu kwayoyin cutar COVID-19 wato cutar COVID-19 ta fito ne daga halittu.

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Reuters ya bayar, ofishin shugaban kasar Faransa ya gabatar da wata sanarwa a ranar 17 ga watan Afrilu cewa, ya zuwa yanzu ba a samu shaidun dake tabbatar da huldar dake tsakanin asalin cutar COVID-19 da aikin nazari dakin gwaji na Wuhan na kasar Sin ba.

A halin yanzu, karin kasashen duniya sun gano mutane masu dauke da cutar COVID-19 da ba su taba ziyartar kasar Sin ba. Alal misali, an gano mutumin da ya kamu da cutar a jihar California ta kasar Amurka wanda bai taba ziyartar yankuna masu fama da cutar, ko yin mu'amala da wadanda suka kamu da cutar ba. Mutane biyu da aka tabbatar da sun kamu da cutar na kasar Iran ba su taba ziyartar kasar Sin ba. An tabbatar da wani mutumin kasar Japan da ya kamu da cutar bayan da ya koma Japan daga Hawaii, shi ma bai ziyarci kasar Sin ba.

Babban direktan hukumar kiwon lafiya ta duniya Tedros Adhanom ya yi kashedi cewa, yin amfani da yaduwar cutar don samun moriyar siyasa ya yi kama da wasan wuta. Ya ce, idan ba a son ganin karin gawawwaki, ya kamata a dakatar da maida batun yaduwar cutar matsayin batun siyasa. A yayin da ake kokarin yaki da cutar, ya kamata a daina yunkurin siyasantar da ita, maimakon haka, a hada gwiwa wajen yaki da ita don kara ceton jama'ar duniya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China