![]() |
|
2020-05-01 15:09:00 cri |
Wani nazarin kwayoyin halittar gado da wasu masanan kasar Faransa suka gudanar ya nuna cewa, cutar COVID-19 da ta bulla a kasar ta Faransa, wata kwayar cuta ce da ke yaduwa a cikin kasar da ba a san asalinta ba ta haddasa, ba daga kasar Sin ko Italiya ba, kamar yadda wasu ke fada a baya.
Masana daga cibiyar Pasteur dake birnin Paris, cibiyar da ta shahara wajen bincike kan cututtuka masu yaduwa, ta fitar da sakamakon nazarin, mai taken, "Gabatarwa da farkon yaduwar SARS-CoV-2 a Faransa" aka kuma wallafa shi a shafin Biorvix.org a ranar 24 ga watan Afrilun wannan shekara.
Masanan sun jera kwayoyin halittu 97 daga samfura da suka tattara daga jikin wadanda suka kamu da cutar a kasar Faransa daga ranar 24 ga watan Janairu zuwa 24 ga watan Maris, inda suka gano cewa, yanayin barkewar cutar a kasar, yana da nasaba da rukunin kwayoyin halittar ko rukunin clade G wanda ba shi da nasaba da kasar Sin ko Italiya. (Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China