![]() |
|
2020-05-03 15:34:08 cri |
A labarin da kafofin yada labarai na kasar Japan suka bayar, an ce, akwai wasu da suka yada labarai na jabu da sunan Mista Tasuku Honjo, cewa wai "mutane ne suka hada kwayar cutar Covid-19", har ma sun ce, Tasuku Honjo ya taba aiki a birnin Wuhan.
A sanarwar da ya fitar, Mista Tasuku Honjo ya bayyana cewa, "yaduwar cutar Covid-19 a fadin duniya ta haifar da wahalhalu da hasarorin tattalin arziki da ba a taba ganin irinsu ba. Sai dai a lokacin da duniya ke fuskantar wahalhalun, an yi amfani da sunana da na jami'ar Kyoto wajen baza jita-jita, abin da ya ba ni mamaki sosai."
Ya kara da cewa, "yanzu lokaci ya yi da ya kamata dukkaninmu, musamman wadanda ke fagen nazarin harkokin kimiyya mu hada kanmu wajen yaki da wannan abokin gabanmu na bai daya. Ya kamata mu kara kokarinmu wajen nazarin hanyoyin kandagarki da dakile yaduwar cutar, tare da tsara shirin da za mu aiwatar a gaba.(Lubabatu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China