Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yiwa 'yan Najeriya 12,004 gwajin cutar COVID-19
2020-04-29 09:36:50        cri

Shugaban cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC, Mr. Chikwe Ihekweazu, ya ce ya zuwa jiya Talata, yawan 'yan Najeriya da aka gwada domin tantance ko suna dauke da cutar numfashi ta COVID-19 ko a'a ya kai mutum 12,004.

Ihekweazu ya bayyana hakan ne a birnin Abuja fadar mulkin kasar, yayin zaman bayyana inda aka kwana, game da ayyukan cibiyar wanda aka watsa kai tsaye ta kafofin yada labaran kasar. Ya ce mahukuntan kasar na aiki tukuru, wajen tabbatar da ingancin ayyukan cibiyar ta NCDC.

Jami'in ya kara da cewa, NCDC na aiki kafada da kafada da wasu dakunan gwaje gwaje dake cikin kasar, domin fadada ayyukanta, matakin da aka dauka domin biyan bukatun da ake da su na yin gwajin cutar a kan lokaci.

Ya ce an shigar da karin wasu dakunan gwaji guda biyu, cikin ayyukan binciken masu dauke da cutar da ake gudanarwa, matakin da ya kara yawan irin wadannan wuraren gwaji zuwa 17. Ihekweazu ya kara da cewa, wadannan matakai ne da aka dauka domin cimma nasarar shawo kan wannan annoba ta COVID-19 a fadin kasar baki daya.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China