Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'an Najeriya sun yabawa matakan da gwamnatin Sin ta dauka wajen yaki da annobar COVID-19
2020-04-24 11:29:39        cri

Jiya Alhamis agogon Najeriya, an yi bikin mika kayayyakin kandagarkin cutar COVID-19 da gwamnatin kasar Sin ta ba kasar. Jakadan Sin dake Najeriya Zhou Pingjian da jami'i mai kula da aikin kandagarkin cutar dake karkashin shugaban kasar Sani Aliyu, da sauran jami'an Najeriya sun halarci bikin.

Yayin bikin, jakada Zhou Pingjian ya nuna cewa, Sin na fatan gabatar da fasahohi da dabarunta ga Najeriya ba tare da boye-boye ba, har ma za ta taimakawa kasar gwargwadon karfinta bisa bukatunta, kuma ya yi imanin cewa Najeriya za ta ga bayan wannan cuta. A matsayin abokan juna da kuma aminai, zumuncin jama'ar kasashen biyu ta fuskar amincewa da ju-na da kuma hadin kansu zai zurfafa tare da samun ingantuwa, yayin da suke tinkarar wannan cuta cikin hadin kai. Yana mai fatan gwamnatin Najeriya ta ba da tabbaci ga lafiya da kuma moriyar Sinawa dake kasar.

A nasa bangaren, a madadin gwamnatin kasar, Sani Aliyu ya gode sosai da taimakon da gwamnatin kasar Sin da kuma kamfanonin Sin dake Najeriya suka ba kasar, ya ce, Sin ce kasar da ta fara bayar da tallafi ga Najeriya, kayayyakin kandagarki da kuma na'urorin taimakon numfashi da Sin ta ba kasar, kuma an riga an raba su ga hukumomin kiwon lafiya na wuraren daban-daban na kasar, ban da wannan kuma, asibitin wucin gadi na jinya da killacewa da kamfanin Sin ya taimaka wajen ginawa a Abuja da dai sauran wurare a shirye suke, kana kuma masu jiyya daga kasar Sin sun ba da taimakon kimiyya da fasaha mai kyau. A cewarsa, ya yi imanin za a ga bayan wannan cuta bisa hadin kai da kasar Sin.

A wannan rana kuma, an mikawa wakilan Najeriya kudin tallafi da kungiyar 'yan kasuwar kasar Sin dake Najeriya ta tattara. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China