Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya: Tabbas hulda tsakanin Najeriya da Sin za ta kara kyautatuwa
2020-04-25 16:43:19        cri

Lawal Sale, wani masani mai sharhi kan harkokin kasa da kasa a Najeriya, ya wallafa wani rahoto mai taken "Annobar COVID-19: Najeriya da Sin suna kokari tare" a jaridar "Peoples Daily" ta kasar, a ranar 23 ga wata, inda ya yi nuni da cewa, ba zai yiyu a gurgunta hadin gwiwar zumunta dake tsakanin kasashen biyu ba, kana goyon bayan junansu ya nuna irin dadadden zumuncin dake tsakaninsu.

A cikin rahoton, Lawal Sale ya bayyana cewa, bayan barkewar annobar, kasar Sin ta dauki matakan da suka dace cikin gaggawa, misali rufe birni da tantance daukacin mutanen da suka yi cudanya da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, wanda ya sa ta yi nasarar hana yaduwar annobar cikin lumana. Ya ce shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ma ya goyi bayan kasar Sin, kuma ita ma gwamnatin kasar Sin da kungiyoyi masu zaman kansu na kasar, sun samar da tallafin kayayyakin kandagarkin annobar ga Najeriya, tare kuma da gabatar da fasahohin dakile annobar da ta samu, duk kuwa da cewa ita kanta tana fama da matsalar.

Ya kara da cewa, Najeriya kasa ce da ta shiga shawarar ziri daya da hanya daya, sannan kuma ta halarci dandalin tattauna hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka. Ya kara da cewa, tun bayan da Najeriya ta shiga shawarar ziri daya da hanya daya, ta samu ci gaba cikin sauri a bangaren gina kayayyakin more rayuwar jama'a. Ya ce ko shakka babu huldar hadin gwiwar moriyar juna dake tsakanin Najeriya da Sin za ta kara kyautatuwa a nan gaba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China