2020-04-28 15:43:42 cri |
Shugaban ya sanar da daukar wannan mataki ne da al'murun jiya Litinin, cikin jawabin sa ga 'yan kasar game da matakan da gwamnati ke dauka, na shawo kan bazuwar cutar numfashi ta COVID-19 a sassan kasar.
Ya ce, yanayi maras dadi da ke wakana a jihar Kano a baya bayan nan, ya tilasa gwamnati rufe jihar Kano ga baki dayan ta.
Rahotanni dai na cewa, an samu yawan mace mace sakamakon dalilan da kawo yanzu, ba a kai ga tantancewa a Kano, jihar da ita ce kan gaba a yawan jama'a a daukacin arewacin kasar. Don haka wasu ke hasashen mai yiwuwa hakan na da nasaba da karuwar masu harbuwa da cutar COVID-19 a jihar. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China