Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cikakken rahoto game da zargin muzgunawa 'yan Afirka mazauna Sin
2020-04-27 13:26:05        cri
An yi ta yada maganganu, da rahotanni, da sakwannin bidiyo, da na sauti, an karanta zarge zarge game da matakan da mahukuntan birnin Guangzhou suka aiwatar, don gane da aiwatar da dokokin dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a birnin.

Birnin Guangzhou na da tarihin karbar baki 'yan Afirka mafi yawa a kasar Sin, inda wani rahoto ke nuna cewa, 'yan Afirkn sama da 320,000 ne ke rayuwa a birnin mai cike da hada hadar kasuwanci.

An dai ji ra'ayoyi mabanbanta, ciki hadda masu razanarwa, wadanda suka ja hankalin al'ummun duniya daban daban, inda kowa ke yin gaba da tasa fahimtar.

Cibiyar bayanai ta Afirka, wato Afri-China Media Centre ko ACMC a takaice, ta yi kokarin tuntubar dukkanin sassan da batun ya shafa, da ma fatan bayyana gaskiyar abubuwa da suka wakana a karon farko, tare da barwa masu karatu damar yanke hukunci. Amma abu mafi muhimmnci shi ne, samar da wannan rahoto, zai taimaka wajen toshe kafofin sabani, tare kuma da ba da damar ci gaba da alaka mai kyau kamar yadda aka saba.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China