Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagogin jami'an lafiyar Sin a yammacin Afirka sun samu horon sanin makamar aiki
2020-04-27 13:20:07        cri
Tawagogin jami'an lafiya na Sin da aka aike zuwa kasashen yammacin Afirka 14, sun samu horo ta yanar gizo daga kwararrun kasar Sin dangane da dakile da kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Karkashin wannan tsari, tawagar kwararrun lafiyar na Sin dake kasar Burkina Faso, a ranar Asabar ta kaddamar da horo ta yanar gizo, a fannin kandagarki da shawo kan annobar ga sauran tawagogin kasar ta Sin masu aiki a sassan yammacin Afirka.

 

Jami'an lafiya 242 daga tawagogin jami'an dake kasashen Burkina Faso, da Nijar, da Guinea-Bissau, da Senegal, da Saliyo, da Cape Verde, da Benin, da Chadi, da Liberia, da Guinea, da Gambia, da Mali, da Togo da Ghana ne suka halarci horon.

Yayin horon, kwararrun sun gabatar da bayanai game dabarun gano cutar numfashi ta COVID-19, da tsarin magance ta, da kare jami'an lafiya, da dabarun tsaftace wurare, da yadda masu aikin jinya za su lura da marasa lafiya. Kaza lika sun amsa tambayoyin game da hanyoyin tallafi da jami'an lafiya suke bayarwa yayin barkewar sabbin annoba a nahiyar Afirka.

Bisa gayyatar gwamnatin Burkina Faso, gwamnatin kasar Sin ta tura tawagar jami'an yaki da annoba zuwa kasar daga Tianjin a ranar 16 ga watan Afirilun nan, domin su agaza wajen ayyukan kandagarki da na shawo kan cutar. Tawagar kwararrun mai mambobi 12, wadda tuni ke Burkina Faso, inda suka gudanar da binciken kimiyya tsawon kwanaki 10, sun kuma samar da horo da tattauna muhimman batutuwa masu alaka da ayyukan su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China