Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka mutu sanadiyyar COVID-19 a Afrika ya kai 1303
2020-04-25 17:21:23        cri
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta Afrika (Africa CDC), ta ce yawan wadanda suka mutu sanadiyyar COVID-19 a nahiyar Afrika ya kai 1,303, yayin da na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 27,852 ya zuwa jiya Juma'a.

Domin shawo kan cutar a yammacin Afrika, kungiyar ECOWAS ta gudanar da wani taro ta kafar bidiyo a ranar 23 ga wata, da nufin tattauna tsarin da yankin zai yi amfani da shi wajen shawo kan annobar.

Shugabanni ko wakilai daga kasashen kungiyar 15 ne suka halarci taron, inda aka zabi shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, a matsayin wanda zai jagoranci aikin yaki da cutar a yankin.

Har ila yau, mambobin kungiyar sun amince da karfafa hadin kai tsakaninsu, domin hada hannu wajen yaki da annobar. Mahalarta taron sun yi imanin cewa, yanayin barkewar cutar ka iya kai wa har karshen watan Satumba, sannan matakan dakile ta da ake dauka ka iya kaiwa akalla har ranar 30 ga watan Yuni.

Jiya Juma'a, ta kasance ranar 1 ga watan Ramadan ga musulmai. Inda wasu daga cikin kasashen Afrika suka ce za su ci gaba da karfafa ayyukan kandagarki da na dakile cutar a cikin watan Ramadan.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya yi kira ga jama'a su kauracewa taron cin abinci da na sallolin jam'i a cikin watan na Ramadan domin dakile yaduwar cutar COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China