Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa CDC: Masu cutar COVID-19 a Afrika sun kai dubu 30 mutane 1,374 sun mutu
2020-04-27 11:05:23        cri
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika wato (Africa CDC) tace, mutanen da suka mutu a sanadiyyar annobar COVID-19 a nahiyar ya kai 1,374 yayin da yawan masu harbuwa da cutar ya kai 30,329 ya zuwa ranar Lahadi.

Hukumar Africa CDC ta fitar da rahoton ta na baya bayan nan a ranar Lahadi inda ta bayyana cewa, an samu rahoton bullar cutar COVID-19 a kasashen Afrika 52 ya zuwa yanzu.

Africa CDC ta bayyana cewa ya zuwa ranar Asabar an tabbatar da mutanen da suka kamu da annobar a nahiyar 29,053, yayin da a ranar Lahadi adadin ya karu zuwa 30,329, an samu sabbin mutane 1,276 da suka kamu da cutar COVID-19 a fadin nahiyar.

Cibiyar Africa CDC ta ce kimanin mutane 9,106 sun warke daga cutar COVID-19 a fadin Afrika ya zuwa ranar Lahadi, inda aka samu sabbin mutanen da suka warke daga cutar kimanin 742 kari kan mutanen da suka warke daga cutar kimanin 8,364 ya zuwa yammacin ranar Asabar.

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta nahiyar ta bayyana cewa, shiyyar arewacin Afrika ne annobar tafi yin kamari a fadin nahiyar ta yin la'akari da adadin masu kamuwa da cutar ta COVID-19, da kuma mutanen da cutar ta hallaka.

A makon da ya gabata hukumar Africa CDC ta jaddada muhimmancin daukar kwararan matakan kandagarki don kariya daga annobar COVID-19 a fadin nahiyar domin dakile yaduwar cutar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China