Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a kafa kyakkyawar makomar Sin da Afirka yayin dakile annobar COVID-19
2020-04-25 15:14:24        cri

A halin yanzu gaba daya adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasashen Afirka ya riga ya kai sama da dubu 25, adadin da yake kara karuwa a kai a kai. Rahoto ya nuna cewa mutane sun kamu da cutar a kusan daukacin kasashen nahiyar, ban da kasashen Comoros da Lesotho.

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, kasar Sin tana samarwa 'yan uwanta dake nahiyar Afirka tallafi gwargwadon karfinta ta hanyoyi daban daban, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin tana son gode wa 'yan uwanta saboda goyon bayan da suka ba ta yayin da take fama da wahalar dakile annobar, haka kuma ya nuna wa al'ummun kasa da kasa cewa, kasar Sin tana sauke nauyin dake wuyanta a bangaren kiyaye lafiyar jama'a a fadin duniya.

A ranar 23 ga wata, wakilan tawagar kwararru masu yaki da annobar COVID-19 ta kasar Sin, suka je ofishin hukumar lafiya ta duniya dake kasar Burkina Faso domin kara fahimtar yanayin kandagarkin annobar a kasar, tare kuma da gabatarwa takwarorinsu na kasar fasahohin da suka samu.

Ban da likitocin kasar Sin wadanda suka dukufa kan aikin dakile annobar a nahiyar Afirka, gwamnati da kamfanonin kasar da Sinawa dake zaune a kasashen Afirka, su ma sun yi kokari matuka wajen samar da kayayyakin kandagarkin annobar ga nahiyar.

Daga ranar 23 zuwa 24 ga wata, kayayyakin kandagarkin annobar COVID-19 da gwamnatin kasar Sin ta samar a mataki na farko, sun isa kasashen Afrika uku da suka hada da Namibiya da Angola da kuma Gabon.

Kasar Sin tana samar wa kasashen Afirka tallafi domin yaki da annobar ta hanyar daukar hakinanin mataki, wanda ya sa ta samu yabo matuka daga manyan jami'an kasashen nahiyar da dama, inda suka bayyana cewa, dadaddiyar zumuntar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka za ta jure jarrabawar da suke fuskantar, kana sassan biyu za su kafa kyakkyawar makoma yayin da suke kokarin dakile annobar tare.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China