2020-04-16 12:59:18 cri |
Kungiyar ma'aikatan ilimi, lafiya da dangogin su a Afirka ta kudu, ko Nehawu a takaice, ta bayyana matukar damuwa, game da yadda ake samun karuwar jami'an lafiya dake harbuwa da cutar COVID-19 a kasar.
Kakakin Nehawu Khaya Xaba, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kusan ma'aikatan lafiya 100 ne suka kamu da cutar COVID-19 a asibitoci masu zaman kan su dake cikin kasar.
Ya ce a makon jiya, an kai ga rufe wani asibiti mai zaman kan sa dake birnin Durban, bayan da mutane 66 dake cikin sa suka harbu da cutar. Kaza lika an samu rahoton rasuwar majinyata 5 dake kwance a asibitin, wadanda aka tabbatar cutar ta COVID-19 ce ta yi ajalin su. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China