Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 20270 sun kamu da COVID-19 sannan 1025 sun mutu a Afrika
2020-04-19 17:01:37        cri
A bisa ga alkaluman da cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa yammacin ranar 18 ga wata, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 ya kai 20,270, yayin da mutane 1,025 sun mutu, kana mutane 4700 sun warke daga cutar a nahiyar.

Kasashen da annobar ta fi shafa sun hada da Masar, Afrika ta kudu, Morocco da Algeria, inda kowacce take da yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar sama da 2,000. Shiyyar arewacin Afrika ne cutar ta fi yiwa illa, inda aka samu mutane 8,900 da aka tabbatar sun kamu da cutar yayin da mutane 745 suka mutu.

Domin cimma nasarar kandagarki da kuma dakile annobar, kasashen Afrika da dama sun dauki matakai masu yawa da suka hada da rufe manyan biranen kasashen da umartar jama'a su dinga amfani da takunkumin rufe fuska a wuraren da ake samun yawan taruwar jama'a.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China