Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin tsakiya na JKS ya kira taron kungiyar jagorancin aikin dakile COVID-19
2020-04-22 21:02:21        cri
A yau Laraba kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya kira taron kungiyar jagorancin aikin dakile annobar cutar COVID-19, inda aka yi nuni da cewa, kasar Sin za ta dukufa domin hana sake barkewar annobar, tare kuma da farfado da tsarin tattalin arziki da zamantakewar al'umma yadda ya kamata, nan gaba za a kara yi wa al'ummun kasar gwada, domin tabbatar da lafiyarsu.

Yayin taron, an jaddada cewa, za a yi kokari domin kyautata fasahar gwada, kana za a kara karfafa aikin hukumar kwastam a iyakar kasa, tare kuma da zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a bangare, ban da haka, za a kara sa ido kan ingancin kayayyakin kandagarkin annobar, tare kuma saukaka aikin fitar da kayayyakin zuwa ketare.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China