Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
G77 da Sin sun fidda sanarwar goyon bayan WHO
2020-04-21 13:33:55        cri
A ranar 19 ga wata, kungiyar kasashen G77 da kasar Sin sun sake fidda wata sanarwa, inda suka nuna yabo dangane da jagorancin da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Sanarwar ta ce, yanzu haka, cutar numfashi ta COVID-19 ita ce babbar matsalar dake gabanmu, kuma abu mafi muhimmanci dake gabanmu shi ne ceton rayukan jama'a. Sanarwar ta yaba wa hukumar WHO dangane da rawar da ta taka wajen yaki da annobar, bisa jagorancin babban darektan hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, ta kuma goyon baya da ma yaba yadda hukumar ta samar da bayanai da tsare-tsare da horaswa ga kasashe masu tasowa wajen yaki da annobar yadda ya kamata.

Sanarwar ta kuma yi fatan cewa, kasashen duniya za su hada kai domin yin kandagarki da hana yaduwar cutar da shawo kan tasirinta. Haka kuma sanarwar, ta yi kira ga kasashen duniya, da su ci gaba da baiwa WHO goyon baya da hadin kai yadda ya kamata. Ta kuma jaddada cewa, cutar numfashi ta COVID-19 abokiyar gabar daukacin bil Adama ce, don haka, idan har ana son ganin bayan wannan annoba, wajibi ne kasashen duniya su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu da inganta dangantakar abokantaka don yaki da annobar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China