Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta taimakawa kasashen Afirka wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19
2020-04-23 14:00:48        cri

Cikin 'yan kwanankin nan, kasar Sin ta ba da taimako na gaggawa ga 'yan uwa kasashen Afirka, sakamakon ci gaba da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a nahiyar. Sin ta tura tawagogin ma'aikatan lafiya zuwa kasashen Afirka a wani mataki na zurfafa hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin kiwon lafiyar jama'a.

Haka kuma, a 'yan kwanankin nan, tawagar ma'aikatan lafiya da kasar Sin ta tura zuwa kasar Burkina Faso ta kai ziyara a asibitoci da dama dake kasar, domin yin musayar ra'ayoyi da masanan sassan kasar.

Jiya Laraba ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Uganda ya kira taron kara wa juna sani kan fasahohin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a tsakanin masanan Sin da Uganda ta kafar bidiyo, inda ya gayyaci ma'aikatan lafiya na lardin Yunan wadanda suka kula da wadanda suka kamu da cutar a birnin Wuhan, da su karin haske, da musayar ra'ayoyi da takwaransu na asibitin zumunci na Sin da Uganda kan fasahohin ba da jinya ga wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19. 

A ranar Talata ne kuma, aka shirya bikin mika kashe na biyu na kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da kamfanonin kasar Sin suka samar wa kasar Mali . A yayin bikin, ministan harkokin kiwon lafiyar kasar Mali Michel Hamala SIDIBE ya nuna godiya ga gwamnati, kamfanoni da jama'ar kasar Sin, a madadin shugaban kasar Ibrahim Boubacar KEITA da ma gwamnatin kasar Mali. Ya ce, goyon bayan da kasar Sin ta baiwa kasarsa wajen yaki da annobar ya nuna zumunci mai karfi dake tsakanin kasashen biyu.

A ranar 20 ga wata kuma, kayayyakin jinya da gwamnatin kasar Sin ta baiwa kasar Gambia ya isa filin jiragen sama na kasa da kasa dake Banjul.

Bugu da kari, a ranar 20 ga wata, rukuni na farko na kayayyakin jinya da kasar Sin ta samar wa kasar Cabo Verde ya isa filin jiragen sama na kasa da kasa dake birnin Praia, fadar mulkin kasa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China