Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Annobar COVID-19 ta yi mummunan tasiri kan tattalin arzkin kasar Sin, inda ya ragu da kaso 6.8 a rubu'in farko na bana
2020-04-17 13:51:39        cri

Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayyana a yau Juma'a cewa, alkaluman GDP na kasar Sin ya tsaya kan yuan triliyan 20.65, kwatankwacin dala triliyan 2.91 a rubu'in farko na bana, inda ya sauka da kaso 6.8 akan na makamancin lokacin bara.

Yayin wani taron manema labarai, hukumar ta ce akwai daidaditon ci gaban tattalin arziki da zaman takewa na kasar a rubu'i na farko, inda kuma ta bayyana barkewar annobar COVID-19 a matsayin gagarumin kalubale.

Alkaluman ya nuna cewa, bangaren bada hidima, wanda ya mamaye kusan kaso 60 na GDPn, ya sauka da kaso 5.2, bangaren masana'antu masu samar da kayayyakin da ake sarrafawa, ya sauka da kaso 3.2, yayin da na masana'antu masu sarrafa kayayyaki ya sauka da kaso 9.6.

Hukumar ta kara da cewa, yanayin yaki da annobar na ci gaba da inganta, inda ake dakile yaduwarta cikin gida, tana mai cewa, ana saurin komawa aiki da samar da kayayyaki, kana ayyukan muhimman kamfanoni na habaka.

Alkaluman da aka fitar yau Juma'a, ta nuna cewa, yanayin samun ayyukan yi ya ingantu kadan a watan Maris, inda yawan rashin aikin a yankunan birane ya tsaya kan kaso 5.9, wanda ya ragu da maki 0.3 daga na watan Fabreru. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China