Hukumar lafiyar Sin: An tabbatar da mutane 30 sun kamu da cutar COVID-19 a jiya Talata
Bisa labarin da hukumar lafiya ta kasar Sin ya fidda a yau Laraba, an ce, ya zuwa jiya Talata, akwai karin mutane 30 da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a babban yankin kasar Sin, ciki hada da mutane 23 da suka shigo kasar daga kasashen ketare, kuma babu wanda ya rasu sanadiyyar cutar a jiya.
Bugu da kari, adadin masu cutar da aka ba da rahotonsu a yankunan Hong Kong da Macao da Taiwan na kasar ya kai 1499. (Maryam)