Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta kaddamar da dandalin karatu ta intanet ga dalibai 'yan kasashen waje
2020-04-21 10:22:47        cri
Kasar Sin ta kaddamar da wani dandalin karatu irin na kasa da kasa, mai suna XuetangX, wanda daya ne daga cikin dandali na farko dake koyar da dalibai a fadin duniya da kwalejoji da jami'o'in kasar suka samar.

Wu Yan, jami'i mai kula da ilimin jami'o'i na ma'aikatar ilimi ta kasar Sin, ya bayyana yayin bikin kaddamarwar cewa, za a samar da kwasa-kwasai kyauta a dandalin ga dukkan sassan duniya, yayin da ake fuskantar annobar COVID-19.

Shugaban Dandalin XuetangX, Wang Shuaiguo, ya ce dandalin na da nufin samar da kwasa-kwasai masu inganci daga gida da waje da samar da nau'o'i daban - daban na karatu ta kafar intanet

Jimilar kwasa kwasai 109 ne aka sanya a intanet cikin harsunan Sinanci da Ingilishi, kuma za a kara wasu manhajojin karatu cikin karin harsuna.

Ma'aikatar ilimi ta kasar ce ta yanke shawarar samar da dandalin ilimin na intanet, da nufin gabatarwa duniya albarkatun ilimi mai inganci na kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China