Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fitar da bayanan jinya na mutane 7 da cutar COVID-19 ta harba a lokacin farko
2020-04-19 20:24:34        cri

Kwanan baya, a karo na farko ne aka fitar da bayanan jinya na mutane 7 da likita Zhang Jixian wadda ta yi gargadin farko kan barkewar annobar a kasar Sin ta tabbatar da sun kamu da cutar, inda likita Zhang ta bude akwatin adana takardun bayanai, ta nuna ra'ayoyin jinya da masanan sassa daban daban suka rubuta.

Daga ranar 26 zuwa ranar 29 ga watan Disambar shekarar 2019, darektan sashen numfashi na asibitin likitancin Turai da gargajiyar kasar Sin na lardin Hubei dake birnin Wuhan zhang Jixian ta tarar da wasu mutanen dake fama da cutar huhu, amma ba tare da gano dalilan janyo cutar ba, sai nan take ta gabatar da rahoton da abin ya shafa ga hukumomin gwamnatin birnin da abin ya shafa, daga nan ta yi gargadin farko kan barkewar annobar kafin sauran likitoci.

Likita Zhang ta bayyana cewa, cibiyar hana yaduwar cututtuka ta unguwar Jianghan ta birnin Wuhan ta dauki mataki cikin gaggawa, bayan da ta samu rahoton da ta gabatar a safiyar ranar 27 ga watan Disambar shekarar 2019, sai nan take wannan rana da yamma, ma'aikatan cibiyar sun je asibitin domin gudanar da aikin bincike kan cutar, a sa'i daya kuma, sun yiwa majinyata dake cikin asibitin gwaji. Ya zuwa ranar 29 ga watan Disambar shekarar 2019, ma'aikatan sun sake zuwa asibitin domin sake yin bincike, ana iya cewa, sun dauki matakai ne a kan lokaci.

Game da hadarin yaduwar kwayar cutar tsakanin mutane, ko ya dace a sanar da jama'a tun da wurwuri, likita Zhang ta bayyana cewa, ana bukatar lokaci kafin a tabbatar da sakamakon nazarin kimiyya, idan ba a tabbata ba, bai dace ba a gayawa saura.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China