2020-04-13 13:05:38 cri |
Kwanan baya, jaridar kwalejin kimiyya da fasaha dake Amurka ta PNAS, wadda ta yi suna sosai a duniya, ta wallafa wani bayani mai take "Phylogenetic network analysis of SARS-CoV-2 genomes" a turanci, inda a ciki ta yi bayani dake nuna cewa, an gano yawancin kwayar cutar COVID 19 a mataki na farko a jikin wadanda suka kamu da cutar daga Amurka da Austriliya.
Masana daga Jamus da Birtaniya, sun hada kai wajen yin nazari, da gabatar da wannan bayani, Kafar CGTN ta zanta da marubucin na farko, kuma masananin kwayoyin halitta dake jami'ar Cambridge dakta Peter Forster ta kafar bidiyo, inda dakta Forster ya tabbatar da cewa, babu wata shaidu dake nuna cewa, wannan kwayar cuta ta samo asali daga birnin Wuhan.
Forster ya bayyana cewa, nazarin da suka yi a wannan karo, don tabbatar da nau'in kwayar cuta na asali.
An ce, daga ran 24 ga watan Disamba na shekarar 2019, zuwa ranar 4 ga watan Maris, masu nazari sun sarrafa kan alkaluman kwayar cutar nau'in SARS-Cov-2 guda 160 da aka tattara daga sassan duniya, inda suka gano sauyar halittun ta guda 3 daga wannan kwayar, wato nau'in A da B da kuma C.
Nau'i na A, ya yi kama da kwayar cuta da aka gano daga jikin jemage da Pangolin, ita ce kuma asalin kwayar, kuma nau'i na B ya samo asali ne daga A, haka ma C ya samu asali daga B. Kididdigar na nuna cewa, nau'i na A da C, an gano yawancinsu a jikin wadanda suka kamu da cutar a nahiyar Turai da Amurka, kana nau'i na B kuma an gano su a Asiya.
Forster ya kara da cewa, kwayar halittun cutar ta farko da aka gano a Wuhan nau'in B ne, amma nau'i na A shi ne asalin wannan cutar, kuma ba a gano su da yawa a Wuhan ba, a maimakon haka, yawancin mutanen da suka kamu da cutar na dauke da kwayar cutar nau'i na B ne a Wuhan, inda nau'in na C ya samo asali daga nan.
An kuma gano cewa, mutanen da suke dauke da kwayar cutar nau'i na A, kusan rabi daga cikinsu daga wurare daban-daban a duniya suke ban da nahiyar gabashin Asiya, kuma yawancinsu suna Amurka da Austriliya, babu mutane da yawa a Wuhan da suke dauke da wannan irin kwayar cuta. Haka kuma, wasu Amurkawa da suka taba zama a birnin Wuhan, an gano cewa, suna dauke da kwayar cutar nau'in na A. (Amina Xu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China