Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta yi karin haske game da matakan yaki da cutar COVID-19 da suka shafi wasu 'yan Afirka
2020-04-13 10:01:09        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yi karin haske game da batun wasu 'yan Afirka, da matakan yaki da cutar numfashi ta COVID-19 suka shafa a lardin Guangdong na nan kasar Sin.

Da yake tsokaci game da hakan a jiya Lahadi, Zhao Lijian ya ce, yayin da kasar Sin ke ci gaba da yaki da yaduwar wannan annoba, gwamnatin Sin na dora muhimmancin gaske ga batun kare lafiyar baki 'yan kasashen waje dake cikin kasar. Tana kuma daukar dukkanin bakin a matsayi guda. Kana ba ta nuna wata wariya ga wasu, ba kuma za ta amince a nunawa al'ummar wata kasa kyama ba.

Jami'in ya ce, mahukuntan lardin Guangdong, na baiwa kula da lafiyar baki masu hada hada a cikin lardin kulawar da ta dace, ciki hada 'yan Afirka mazauna lardin. An kuma tsara matakai na musamman, domin tabbatar da kare lafiyar su gwargwadon iko, wanda hakan ya ba da damar ceton rayukan wasu 'yan Afirka da suka sha fama da matsanancin yanayi na rashin lafiya a lardin.

Cikin matakan da gwamnatin lardin ta dauka dai, akwai samar da hidimar kula da lafiya ba tare da nuna wariya ba, da kebe wasu otal otal a matsayin masauki ga bakin da za a sanya ido kan su, domin tabbatar da ba sa dauke da wannan cuta. Kaza lika an samar da rangwamen farashi ga wadanda ke cikin hali na matsi.

A daya bangaren kuma, an tanaji tsarin tattaunawa da babban jami'in ofishin jakadanci dake birnin na Guangzhou, fadar mulkin lardin Guangdong, a wani mataki na kawar da duk wani yanayi da ka iya zama nuna kyama ne ga bakin dake lardin.

Zhao Lijian ya kara da cewa, Sinawa na kallon al'ummun Afrika a matsayin 'yan uwa abokan hulda, a lokuta na dadi da na wahala. Kuma kawancen dake tsakanin sassan biyu ba zai yanke ba, duba da karfin da yake da shi bisa tarihi.

Daga nan sai jami'in ya jaddada matsayin gwamnatin kasar Sin, na ci gaba da baiwa abokai 'yan Afirka dukkanin kulawar da ta kamata a yayin da suke cikin kasar Sin. Har ila yau, jami'in ya ce ma'aikatar harkokin wajen Sin, za ta yi aiki kafada da kafada da mahukuntan lardin Guangdong, za ta kuma ci gaba da jin ta bakin baki 'yan Afirka mazauna lardin domin kare bukatun su bisa doka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China