Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministocin kudin G20 da gwamnonin bankunan kasashe mambobin kungiyar za su gana ranar Laraba
2020-04-13 09:07:14        cri
Ministocin kudin kasashe mambobin kungiyar G20, da gwamnonin bankunan kasashen kungiyar, za su yi wata ganawa a ranar Larabar dake tafe, domin tattauna batutuwa masu nasaba da kalubalen da cutar COVID-19 ta haifar.

A cewar kamfanin dillancin labarai na "Saudi Press", bisa al'ada a kan gudanar da taron na watan Afirilun ko wace shekara ne a birnin Washington D.C. na Amurka, a gefen taron asusun ba da lamuni na duniya IMF, da taron masu ruwa da tsaki na babban bankin duniya.

A yayin taron su na ranar 31 ga watan Maris da ya gabata, sassan biyu na kungiyar G20, sun amince da wani cikakken tsari da ya dace a bi, wajen shawo kan mummunan tasirin da cutar COVID-19 ta haifar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China